Fati Washa ta lashe kyautar gwarzuwar jaruman Hausa a Birtaniya - MY CITY NEWS NG

Cool News from Nigeria cities

ads

test banner

Breaking

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Sunday, November 3, 2019

Fati Washa ta lashe kyautar gwarzuwar jaruman Hausa a Birtaniya

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Fatima Abdullahi da ake kira Fati Washa ta lashe kyautar gwarzuwar jaruman Hausa a wani kasaitaccen bikin fina-finan Afirka da aka gudanar a Birtaniya.
Image result for fati washa
An sanar da Washa ne a matsayin gwarzuwar jaruma a taron karrama 'yan Fim da aka gudanar ranar Asabar a birnin London.
Bikin wanda ake kira Afro Hollywood Awards ya shafi karrama jaruman fina-finan harsunan Najeriya guda uku Hausa da Yoruba da Igbo da kuma na Inglishi a sassan kasashen Afirka,
Fati Washa ta lashe kyautar ne saboda rawar da ta taka a Fim din 'Sadauki.'
Jarumar ta doke Aisha Aliyu Tsamiya a Fim din da ta fito "Jamila" da kuma Halima Yusuf Atete da ta fito a "Uwar Gulma"
Rahama Sadau ta wallafa hoton bidiyo a shafinta na Instagram, lokacin da Washa ta ke karbar kyautar, inda ta bayyana farin cikinta da godiya.
Ita ma Washa ta sake wallafa bidiyon a shafinta na Istagram.
Washa ta ce ta sadaukar da wannan kyautar ga masoyanta tare da gode ma su, kamar yadda ta wallafa a shafinta na Facebook da ba a tantance ba.

Karo na 23 ke nan da ake gudanar da bikin karrama 'yan fim din wanda jaridar African Voice Newspapers a Birtaniya da gidauniyar Esther Ajayi da Ned Nwoko ke daukar nauyi.
Wadanda ke shiryawa da daukar nauyin bayar da kyautar a Birtaniya sun ce Sama da fina-finai 500 ne daga Afirka suka shiga gasar wacce aka fara a 1996.

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad

Responsive Ads Here