AMERICA TA DAU ZAFI - MY CITY NEWS NG

Cool News from Nigeria cities

ads

test banner

Breaking

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Sunday, November 3, 2019

AMERICA TA DAU ZAFI

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa yanzu zai koma da zama ne a Florida, maimakon inda aka fi sani, wato Trump Tower da ke New York.

Image result for DONALD TRUMP4
Ya ce masu mulki na birnin New York suna matsa masa duk kuwa da cewa yana biyan haraji na miliyoyin daloli.
An haifi Trump ne a birnin New York amma a cikin kwanakin nan alamu sun nuna cewa ya fi zama a gidansa da ke Mar-a-Lago a wani wuri da ake kira Palm Beach.
Shugaban, wanda dan jam'iyyar Republican ne, ba ya ga-maciji da gwamnan New York Andrew Coumo da magajin garin birnin Bill de Blasio - wadanda dukkanin su 'yan jam'iyyar Democrats ne.

Kuma dukkanin su sun yi maraba da labarin tashin Donald Trump din daga New York zuwa Florida.
A wani sakon twitter Mr De Blassio ya ce wa Trump 'Umma ta gaida aisha.'

Mr Trump bai taba wallafa bayanan kudin da yake samu, ko kuma bayanan biyan kudin harajinsa ba.
Trump ya mallaki makeken gidan ne na Mar-a-Lago tun a shekara ta 1985, kuma yana yawan zuwa gidan ko bayan zaman sa shugaban kasa.
Shugaban na son sake tsayawa takara a zaben shekara mai zuwa, inda ya bayyana a fili cewa yana so ya ci gaba da zama a fadar White House nan da shekara 5 masu zuwa.

Ya ce har gobe yana son birnin New York, amma "Abin takaici, duk da cewa na biya haraji na miliyoyin dala ga hukumomin birnin, da na jiha, 'yan siyasa suna ci gaba da tsangwama na"
Jaridar The New York Times ta ruwaito cewa shugaba Trump da mai-dakinsa Melania sun nemi takardar izinin zama a Florida, cikin watan Satumba.
Bayanan da jaridar ta samu sun nuna cewa sauran gidajen da Trump ke zama sun hada da mai lamba 1600 Pennsylvania Avenue (the White Houe) da kuma wani wurin da yake zuwa buga wasan golf da ke a Bedminister a jihar New Jersey.
Asalin gidan da Mr Trump ya fi zama a ciki shi ne wanda ke a wani bangare na Trump Tower a Manhattan, inda yake zaune tun shekarar 1983. Sai dai babu tabbas ko zai ci gaba da zama a cikin sa.


Gidan talabijin na NBC News ya ce tun bayan hawansa mulki, shugaba Trump ya yi kwanaki 99 ne a makeken gidansa na Mar-a-Lago, yayin da ya yi kwana 20 kacal gidansa na Trump Tower.
Fadar White House ba ta ce komai ba game da dalilan da suka sanya Trump din ya canza wurin zama, sai dai jaridar New York Times ta ruwaito wani na kusa da shugaban na cewa ya yi hakan ne bisa dalilan da suka jibanci biyan haraji.
A cikin watan Oktoba ne dai wani alkali ya umurci Trump da ya mika bayanan kudaden da ya samu, wadanda za a iya biya wa haraji ga masu bincike na birnin New York.
Wannan hukunci zai taimaka a binciken da ake yi kan kudaden toshiyar baki da ake zargin an biya wasu mata biyu, wadanda suka yi ikirarin cewa Trump ya yi lalata da su.

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad

Responsive Ads Here