Zaben cike gurbi: Masana'antar Kannywood ta taya gwamna Ganduje murnar samun nasara - MY CITY NEWS NG

Cool News from Nigeria cities

ads

test banner

Breaking

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Wednesday, March 27, 2019

Zaben cike gurbi: Masana'antar Kannywood ta taya gwamna Ganduje murnar samun nasara

Dandalin masana'antar Kannywood ta fina-finan Hausa, ya taya gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, murnar samun nasara ta lashe zaben gwamnan jihar Kano karo na biyu da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Maris.
 Zaben cike gurbi: Masana'antar Kannywood ta taya gwamna Ganduje murnar samun nasara
Mun samu cewa, dandalin masana'antar Kannywood ta fina-finan Hausa, ta yi tarayya da jam'iyyar APC wajen taya gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, murnar samun nasarar tazarcen kujerar sa a karo na biyu. Zaben cike gurbi: Masana'antar Kannywood ta taya gwamna Ganduje murnar samun nasara Source:
Depositphotos Majiyar jaridar citynews.ng ta ruwaito cewa, wasu daga cikin fitattun jaruman Kannywood sun taya gwamna Ganduje murnar samun nasara ta hanyar watsa sakonni a shafukan su na zaurukan sada zumunta. Ire-iren mashahuran jaruman Kannywood da suka taya gwamna Ganduje murnar samun nasara a shafukan su na dandalan sada zumunta sun hadar Ali Nuhu, Fati Shu'uma da kuma Baban Chinedu duk cewar ba ya da wata alkibla ta akidar siyasa.
Gwamna Ganduje ya sha da kyar yayin lallasa babban abokin adawar sa na jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf, inda ya ba shi tazara ta kimanin kuri'u 8,982 kacal kamar yadda hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC ta bayyana. KARANTA KUMA:
Ba za mu bari jam'iyyar adawa ta kusanci jagoranci ba a Majalisar tarayya - Oshiomhole Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, dandalin Kannywood ya yi tarayya da wasu daga cikin al'ummar jihar Kano wajen taya gwamna Ganduje murnar samun nasarar tazarce yayin babban zaben da aka gudanar a karshen makon da ya gabata.

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad

Responsive Ads Here